Wata budurwa mai suna Maida Aliyu, ta sanar da wani abin mamaki da akuyarta da ‘yar uwar mahaifiyarta ta bata, cewa ta sake yin abin mamaki game da haihuwar awaki da take yi mai yawa.
A cewarta; wannan akuya tun a shekarun baya tana haihuwar ‘ya’ya biyu, daga baya kuma ta sake haifar ‘yan uku. Amma a wannan karon abin ya dauki hankalin jama’a domin akuyar ta haifi ‘yan biyar.
- Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
- NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
Daga cikin awakin da ta haifa uku maza ne sai kuma biyu jinsin mata.
Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.
A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su.
Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp