“Wannan wani muhimmin lokaci ne ga dangantakar dake tsakanin Sin da Brazil a tarihi” ” Bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa fiye da 30″ “An bude sabon babin kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu a shekaru 50 masu zuwa”…Ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jiya Laraba a kasar Brazil, ya jawo hankalin kafofin yada labarai na kasa da kasa sosai.
A yayin tattaunawarsu a wannan rana, shugabannin kasashen biyu sun cimma daidaito kan ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashensu a nan gaba. A matsayinsu na jagora a tsakanin kasashe masu tasowa, dangantakar dake tsakanin Sin da Brazil ta riga ta zarce matsayin wadda ake yi a tsakanin wasu kasashe biyu, kuma tana taka rawa mai muhimmanci wajen kyautata harkokin mulkin duniya. Daga bayar da ra’ayin bai daya a fannoni guda shida tare da nufin inganta warware rikicin Ukraine a siyasance, zuwa yin kira da a tsagaita bude wuta tsakanin Falasdinu da Isra’ila, da aiwatar da “shirin samar da kasashe biyu”. Kasashen Sin da Brazil duka suna bin ra’ayin kasancewar bangarori da dama cikin al’amuran kasa da kasa bisa gaskiya, kana suna dagewa kan yin magana da tafiyar da harkoki cikin adalci.
A wannan karon, Sin da Brazil sun bayyana baki daya cewa, za su ci gaba da yin hadin gwiwa ta kut-da-kut a cikin tsare-tsare na bangarori da dama, kamar MDD, da G20, da BRICS da dai sauransu, domin tinkarar kalubalen da suka shafi yunwa da fatara, rikice-rikicen yanki, sauyin yanayi, da kuma tsaron yanar gizo da dai sauransu.
Muna iya yin imani da cewa, yayin da kasashen Sin da Brazil suka kara hada kansu, za a iya tabbatar da moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, kuma za a kara karfi wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Bilkisu Xin)