Ciwon Kansa na iya kama kowane bangare na jikin Dan’adam, hakan na faruwa ne idan jinin wurin ya gaza yin aikinsa, wanda yakan jawo wa jiki kasa aikin da ya kamata ya yi.
Har ila yau a kan iya amfani da maganin Kansa a sha a warke, domin kuwa an yi wa mutane da dama sun samu lafiya, sun kuma ci gaba da rayuwarsu kamar sauran mutane.
- Yadda Aka Gudanar Da ‘Tattakin Zaman Lafiya’ A Jihar Zamfara
- Sin Na Maraba Da Goyon Bayan Duk Wani Kokari Da Zai Taimaka Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya
Mene ne asalin ciwon Kansa?
Kansa ba wai cuta ce guda daya ba, domin ta rabu gida daban-daban, sannan wannan cuta takan iya farawa daga huhu, nono, ciwo ko kuma ta jini. Kazalika, a kan iya kamuwa da wannan cuta ta gurare da dama; amma hanyoyin yaduwarta sun banbanta.
Ta wadane hanyoyi cutar Kansa ke farawa?
Kowace kwayar halitta ta jikin mutum akwai aikin da take yi, asalin kwayar halittar ta kan kasu kashi-kashi; suna mutuwa idan aka fitar da su ko kuma suka lalace, sai wata kwayar ta maye gurbinsu. A irin wannan lokaci ne, Kansar ke samun gurin zama sai ta zuba tata kwayar halittar ta kori asalin kwayar halittar da ke jikin Dan’adam, wanda hakan ke jawo matsaloli a sassan jikin da Kansar ta kama.
Saboda haka, kwayar cutar Kansa; ta kan watsu a sauran sassan jiki, misali Kansar huhu ta kan tafi cikin kasusuwa ta girma, a yayin da kwayar ta yadu; ana kiranta da suna ‘meh-TAS-tuh-sis’, ita kuma Kansar huhu idan ta tafi cikin kasusuwa; ana kiran ta da suna ‘Lung Cancer’ a turance. A bangaren likitoci, kwayar cutar Kansar da ta shiga cikin kashi; daidai ta ke da ta huhu, sai dai idan ta yadu a cikin kashin.
Banbance-banbancen cutar Kansa:
Wata Kansar ta kan yadu ne cikin gaggawa, yayin da kuma wata ta ke yaduwa a hankali a hankali, sannan kowacce ana iya yin maganinta ta hanyoyi daban-daban, wata ta hanyar tiyata kadai za a iya samun waraka; wata kuma ta hanyar shan magani.
Idan mutum yana dauke da Kansa, likita ya kan yi kokari wajen gano irin Kansar da yake dauke da ita. Mutanen da ke da cutar Kansa, ana yi musu magani ne gwargwadon irin yanayin wadda suke dauke da ita.
Wane matsayi cutar Kansa ta taka?
Duk wanda ke dauke da wannan cuta ta Kansa, likita zai so sanin matakin da ta kai, daga inda ta fara ana kiran sa a turance ‘Cancer Stage’, sannan matsayin da Kansar ta ke shi ne zai taimaka wajen sanin maganin da za a dora mai dauke da lalurar a kai.
Kowace irin Kansa, akwai gwajin da ake yi domin gano matasayin da ta kai. A dokar gwajin matakinta na farko da kuma mataki na biyu, na nuna Kansar ba ta yi karfi sosai ba. Mataki na uku da na hudu kuma yana nuna ta yadu sosai. Mataki na hudu shi ne makura wajen yaduwar ta.
Alamomin 20 Na Kamuwa Da Cutar Kansa:
1- Shashsheka da karancin numfashi
2- Tari da ciwon kirji, alama ce ta Kansar huhu ko ta bargo ciwon kirjin kan kasance daga kirjin zuwa kafada, sannan ya sauko zuwa hannu
3- Zazzabi da saurin kamuwa da ciwo, hakan na faruwa ne dalilin asalin kwayar halittar jinin mutum ta tabu
4- Fama wajen hadiye abu, wannan na nuni da an kamu da wannan cuta
5- Futowar kurji me ruwa a wuya, hammata da kuma gwiwa
6- Yawan zubda jini
7- Kasala da yawan gajiya
8- Kumburin ciki
9- Rashin sha’awar abu da kuma daukewar dandano
10- Ciwon ciki da mara
11- Fitar jini daga dubura
12- Rama lokaci guda
13- Yawan ciwon ciki
14- Nono ya yi ja ya kumbura alama ce ta ‘breast cancer’
15- Canjawar kan nono
16- Nauyi da kuma ciwo na fitar hankali a lokacin al’ada, wannan ita ma alama ce ta ‘uterus cancer’, ana bukatar yin hoto (transbiginal)
17- Kumburin fuska
18- Canjawar farce, zai iya kasancewa ‘lung cancer’, idan kuma ya kode ya yi fari to ‘liber cancer’ ne
19- Ciwon baya a bangaren dama, yana nuni da ‘liber cancer’ ko ‘breast cancer’
20- Fesowar kuraje a jikin mutum
Amma sai an je asibiti an ga likita kafin a tabbatar.
Daga taskirar Muhammad Mubarak Bala