Masu sha’awar yawon bude ido a cikin kasar Sin sun ziyarci sassa daban daban na kasar, albarkacin hutun kwanaki 3 na sabuwar shekarar 2023, inda adadin yawon shakatawa a cikin kasar ya kai kimanin miliyan 52.7, adadin da ya karu da kaso 0.44 bisa dari, sama da na shekarar da ta gabata.
Alkaluman hukumar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin, sun nuna yadda harkokin yawon shakatawa a lokacin hutun sabuwar shekarar ya samar da harajin da ya kai kudin Sin sama da Yuan biliyan 26.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.8, adadin da ya karu da kaso 4 bisa dari kan na shekarar bara.
Kaza lika, alkaluman ma’aikatar sun nuna yadda kasuwar harkokin raya al’adu da yawon shakatawa, ta ci gaba da daidaita bisa tsari, a yayin hutun da aka kammala a jiya Litinin.
Har ila yau, alkaluman sun nuna cewa, harkokin sufuri matsakaita da masu dogon zango, na kara farfadowa a kasar Sin, kuma wasu cibiyoyin cinikayya a fanni dake kan yanar gizo, sun bayyana samun karuwar abokan hulda dake sayen tikitin su, domin yin tafiye-tafiye tsakanin larduna daban daban, da yawon shakatawa tsakanin kasashe, duk a lokacin na hutun sabuwar shekara. (Saminu Alhassan)