Batun yawan kudaden da Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya ke karba na ci gaba da yamutsa hazo a Nijeriya.
Wannan na zuwa ne bayan kalaman tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo kan albashin nasu.
- Nazarin CGTN Ya Bayyana Yadda Wasu Mutanen Duniya Suka Soki EU Game Da Takkadamar Cinikayya Tsakaninta Da Sin
- Tawagar JKS Ta Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Kasar Rwanda
Tsohon shugaban na Nijeriya, ya bijiro da batun yawan albashin ‘yan majalisa ke karba, inda ya yi zargin cewa su ke yanka wa kansu albashi mai tsoka.
A martaninsa, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila daga Jihar Kano, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, ya ce ba wasu kudade ba ne ‘yan majalisar ke samu da har zai zama wani abin cece-kuce.
“Kudin da ake karba na albashi a wata bai kai Naira miliyan daya ba, idan an yi yanke-yanke ya kan dawo kamar Naira dubu dari shida da dan wani abu a matsayin albashi,” in ji Kawu.
‘Yan Nijeriya dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da albashi da alawus-alawus da ‘yan majalisun ke karba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp