Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaben mazabar tarayya ta Tudun Wada/Doguwa a Jihar Kano.
An ayyana Doguwa ne a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala zaben da aka gudanar ranar Asabar a wasu rumfunan zabe na mazabar.
- Wang Yi Da Qin Gang Sun Gana Da Ministar Harkokin Wajen JamusÂ
- Dan Takarar NNPP Ya Kayar Da Dan Majalisa Mai Ci A Fagge
Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Sani Ibrahim ne, ya sanar da sakamakon zaben, inda ya ce Doguwa na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 41, 573.
Babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar NNPP, Yushau Salisu ya samu kuri’u 34,831 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 2,111.
LEADERSHIP ta ruwaito tun da farko an bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu kafin INEC ta soke hukuncin da ta yanke, inda ta ce jami’in zaben mazabar ya bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben cikin dimuwa.
Sakamakon haka hukumar zaben ta soke zabukan da aka gudanar a wasu rumfunan zabe na mazabar tarayya tare da shirya sake gudanar da wani zaben.