Ana ci gaba da mayar da martani a kan kiran da Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago ya yi na neman a soke Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON a kan ikirarinsa na yadda hukumar ta tafiyar da harkokin aikin Hajjin wannan shekarar.
Martani na baya-bayan na ya fito ne daga wasu Alhazan jihar, inda suka ce Gwamnan ya nuna son rai a kalamansa kuma ba da yawun alhazan Jihar Neja da ma na Nijeriya gaba daya ya yi wadanna maganganun ba.
“Ba da yawunmu gwamnan ya yi kalaman ba, in ka lura ma masaukan da gwamnatin jihar ta kama mana a Makkah yana can bayan gari ne nesa da Harami.
“Ba mu samun zuwa gudanar da sallolin mu a masallacin harami saboda nisa amma gwamnan ya kawar da kansa daga wannan mastalar yana magana a kan Tanti masu alfarma (Tent A) a Muna saboda shi ne ta shafa ba sauran Alhazai abin yan shafa ba” in ji wani Alhaji mai suna Halilu Usman daga jihar.
A martaninsa, Jami’in watsa labarai na hukumar Alhazan Jihar Neja, Jibrin Usman Kodo ya bayyana cewa, lallai masaukan alhazan jihar a Makkah ya yi nisa da Harami amma sun samar da motoci 7 da ke zirga- zirgar kai Alhazai zuwa masallacin Harami da dawo da su domin gudanar da ibadunsu. Ya bayyana haka ne a takardar manema labarai da ya sawa hannu a ranar Alhamis a Makkah.
Amma kuma a wani bincike, wakilinmu ya ga yadda wasu Alhazan Jihar Neja ke taka sayyada daga masaukinsu zuwa Harami,: “Motoci biyu kawai ke zirga-zirgar daukar Alhazai suma ba akai-akai ba.
“Kamar yadda ka gani, da yawa cikinmu takawa muke yi na wajen awa biyu zuwa da dawowa Harami shi ya sa wadanda basu da karfi suke zamansu a otal.
“Ta yaya jihar da ta kasa samar wa da alhazanta ingantaccen masauki kusa da Harami za ta nemi a karbe harkokin gudanar da aikin hajji gaba daya daga Hukumar NAHCON?,” tambayar da wani Alhaji kuma dan kasuwa mai suna Abubakar Umar ya yi wa waklinmu ke nan.
Haka kuma kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a kan harkokin aikin hajji da dama sun yi fatali da kalaman Gwamna Bago na a soke hukumar aikin Haji ta Nijeriya NAHCON, inda suka nuna cewa, kiran ba shi tattare da wata hikima.
Kungiyar ‘Independent Hajj Reporter, IHR’ ta nuna rashin amincewa da kalaman na Bago a cikin sanarwa da ta fitar ranar Litinin inda shugabanta na kasa Ibrahim Muhammad ya sanya wa hannu. Kungiyar ta kara da cewa, a dokoki na duflomasiya, kasar Saudiya tana hulda ne da hukumar Alhazai daya tak daga kowace kasa ba hukumomin Alhazai ba, ‘Wannan kira na Bago na nufin kasar Saudiya za ta yi hulda da hukumomin Alhazai 36 ke nan daga Nijeriya, abin kuma da ba zai yiwu ba kenan” in ji ta.
Haka kuma wata kungiyar ‘yan jarida masu kula da aikin hajji mai suna ‘Media Awareness Initiatibes for Hajj (MAI-HAJJ)’ ta yaba wa hukumar NAHCON a kan yadda ta gudanar da harkokin aikin hajji a wannan shekarar, musamman a bangaren abin da ya shafi masaukai da abincin da aka ciyar da Alhazai a Masha’.eer (Mina and Arafat).
Kungiyar ta bayyana haka ne a takardar sanarwar da ta raba wa manema labarai ranar Juma’a 28 ga watan Yuni 2024, wanda mataimakin shugabanta na yankin arewa Uwais Abubakar Idris da jami’inta na watsa labarai, Malam Kabiru Yusuf suka sanya wa hannu.
“Yawancin alhazan da ‘yan jaridarmu suka tattauna da su sun nuna yadda aka ci abinci har ana zubarwa a Mina da Arafat saboda yawan abincin da NAHCON take ciyar da aalhazai.,” in ji kungiyar.
Kungiyar ta kuma yi watsi da kalaman Gwamnan Nija, ta ce ba a taba samun aikin hajin da ba bu mastala ba a duk duniya, amma dole a yaba wa NAHCON musamman shugabanta Malam Jala Ahmed Arabi.