Kwanan baya shugaban kasar Azerbaijan Ilham Heydar oglu Aliyev ya yi zantawa da wakilin CMG, inda ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar hulda tsakanin kasarsa da kasar Sin, kuma ya yaba da shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar, kana ya sake nanata cewa, Azerbaijan tana nacewa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, tare kuma da goyon bayan dunkulewar gabobi biyu na zirin Taiwan.
Shugaba Aliyev ya kara da cewa, yana yin kokarin raya kasarsa ta Azerbaijan, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashe makwabta, haka kuma Azerbaijan za ta kara bude kofarta ga waje.
Haka zalika, yana mai cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Azerbaijan da kasar Sin zai taka muhimmiyar rawa wajen jigilar kayayyaki tsakanin kasashen yamma da na gabashi. (Mai fassara: Jamila)