Gwamnatin Jihar Legas ta kori alkalin wata kotu, Ishola Adeyemi, wanda ake zargin yayanke danyen hukunci na raba auren wani da ya kawo kara, Olayemi Ayeni kuma ya koma ya dirka wa matar ciki.
Ayeni ya bayyana yadda Alkalin, Adeyemi, ya rabasa da matarsa, Doyin Okububi, sannan kuma ya hana shi damar rike yaransa. Inji rahoton jaridar labarun hausa.
Ayeni ya bayyana cewa, Matarsa, Doyin ta daina ganin kimarsa tun lokacin da ya bata Naira Miliyan 5 ta fara kasuwanci.
Daga bisani ma ta kwashe kayanta ta bar gidana sannan ta kama wani gida kusa da ni.
Hakan yasa na kai Kara kotu, Ina tunanin aurenmu zai samu sasanci ta wannan hanyar, Kawai sai alkalin ya yi gaggawar raba aurenmu sannan ya dirka mata ciki bayan watanni 3 da raba aurenmu.
“Abinda ya fi damuna shi ne, ya hana ni damar ganin yarana.
“yaci gaba da kula da yarana da kasuwancin da na ba tsohuwar matata jari. Ya hanani damar ganawa da yarana sannan ya dirkawa matata ciki tare da tura ni gidan yari,” inji mutumin.