Alkaluman awon sauyin tsadar kayayyaki da na hidimomi na kasar Sin ko CPI ba su sauya ba a watan Satumba, sabanin yadda suka kasance a makamancin lokaci na shekarar bara.
A cewar hukumar kididdigar kasar ta Sin NBS, bisa wa’adin wata-wata, alkaluman na CPI sun daga da kaso 0.2 bisa dari daga na watan da ya gabaci Satumba.
- Xi Ya Yi Kira Ga Jiangxi Da Ya Rubuta Nasa Babin A Kokarin Zamanantar Da Kasar Sin
- Shugabannin Kasashen Duniya Na Cike Da Kyakkyawan Fata Game Da Taron Raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya
Kaza lika, muhimmin jigo na awon CPI, ban da farashin abinci da makamashi, ya daga da kaso 0.8 bisa dari a shekara a watan na Satumba, ko da yake yanayin karuwar ba ta sauya ba idan an kwatanta da watan Agusta.
Har ila yau, matsakaicin CPI din na Sin, tsakanin watan Janairu zuwa Satumban bana, ya karu da kaso 0.4 bisa dari a shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)