Alkaluman farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin (CPI), wanda ke auna matakin hauhawar farashin kayayyakin, sun daga da kaso 0.5 bisa dari a watan Janairu.
Adadin ya karu ne kan kaso 0.1 bisa dari da ya kasance a baya, galibi saboda hutun bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, a cewar hukumar kididdigar kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)