Abdullahi Abacha, wanda shi ne da na biyun karshe ga tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Janar Sani Abacha, ya rasu yana da shekara 36 a duniya.
Iyalin Abacha sun tabbatar rasuwarsa a yau Asabar, inda suka ce Abdullahi ya rasu ne cikin dare a gidansu da ke titin Nelson Mandela a Abuja, babban birnin tarayya.
- Sojoji Sun Kashe Mutum 1, Sun Ceto 14 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna
- Ra’ayoyin PDP, PRP Da SDP Kan Gudanar Da Zabe A Kano
“A daren jiya fa lafiyarsa kalau ya kwanta, amma yau da safe sai gawarsa a ka samu.
“Ya rasu cikin kwanciyar hankali a cikin barcinsa,” in ji wata majiya daga iyalin Abacha.
Leadership Hausa ta tattaro cewa za a yi jana’izarsa da misalin karfe 4 na yamma a babban masallacin kasa da ke Abuja.
An haife shi a shekarar 1987, marigayin yana daya daga cikin yara tara da marigayi shugaban soji ya bari.
Tuni ‘yan uwa da abokan arziki suka shiga alhini da gaisuwar rasuwar matashi a kafafen sada zumunta.