Tumatir da barkono da albasa da sauran kayan miya na neman gagaran ‘yan Nijeriya, musamman a Jihar Kano, saboda tsada da hauhawar farashi, a wani bincike da aka gudanar.
Yayin da ake sayar da kwano guda na tumatur a kan kudi naira 5,000, tattasai kuma naira 10,00, attarihu naira 3,500, yayin da jama’a ke sayan kwanon albasa kan naira 2500.
- Nazari Game Da Rayuwar Muhammadu Buhari
- Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba
Wani mai sayar da kayan miya a Kano, Umar Ali ya shaida cewa kwandon tumatur ya yi tsada, inda ake sayar da shi daga kan naira 65000 da 70,000, ko da kuwa a kasuwar ‘Yan Kaba ne, wani babban kasuwar sayar da kayan miya da ke Kano, yayin da kuma buhun attarihu ake sayar da shi sama da naira 120,000.
“Yanzu na sayo wadannan kayan, komai ya yi tsada, saboda wasu kwastomominmu suna daurewa su saya a haka,” Ali ya shaida.
Shi kuwa wani ma’aikacin jinya a asibitin Malam Aminu Kano, Bukar Zanna ya ce yanzu shi kam ya koma sayen busasshen kayan miya domin yin abinci.
Ya ce, matarsa tana kokarin amfani da kayan sa dandano ta hade da busasshen kayan miya domin yin abun da za su ci.
“Ni kam na daina sayen danyen kayan miya saboda tsananin tsada. Na koma sayen busasshe domin yin miyan abincin da muke ciki,” ya tabbatar.
Abubakar Danzaria shi kuma cewa ya yi a karshen mako ya sayi tumatur da albasa da tattasai da tarihu na naira 7,500, amma kwanaki biyu kacal matarsa ta shaida masa cewa kayan miyan sun kare.
Masu sayar da kayayyaki dai na danganta hauhawar farashin da karancin noman kayan miyan da a farkon damina a wasu sassan Kano da kuma tsadar da ake samu wajen jigilarsu daga yankunan da ake noman tumatur kamar Zariya, Gombe da Jos.
Shugaban kungiyar masu sayar da tumatur na Jihar Kano (TOGAN), Sani Danladi Yadakwari ya shaida wa ‘yan jarida cewar karancin noman kayan miya shi ne ke janyo tsadar kayan miyan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp