A wani taron gaggawa da ‘yan kasuwan Jihar Kano, gwamnan Kabir Yusuf ya misalta cewa al’umman jihar na fama da matsatsin rayuwa da fatara mai muni.
Ya shaida wa ‘yan kasuwan cewa, “Akwai fatara a Kano kuma dole ne mu nemo mafita domin tsaida mutuwar. Al’ummarmu da suke fadi su mutu ko su kamu da rashin lafiya. Mun sani kuna iya bakin kokarinku a matsayinku na ‘yan kasuwa, amma ba wai kuna yin iyaka abun da ya dace ku yi ba kenan.
- Shugaban Karamar Hukuma A Kano Ya Yi Murabus, Wani Kuma Ya Fice Daga APC Zuwa NNPP
- Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta
“Dole mu hada karfi da karfe waje guda mu nemo mafita, a matsayina na gwam-na da mataimakina ba mu bukatar komai daga wajen kowa. Kawai abun da muke da bukata shi ne ku zo ku taimaka mana domin mu taimaki talakawanmu.”
Gwamna Yusuf ya bukaci ‘yan kasuwan da su taimaka wa kokarin gwamnatin ji-har, ya ce, “Ina rokonku da ku nemi hanyoyin rage farashin kayan masarufi domin saukaka wa jama’a.
“Kano cibiyar kasuwanci ce a Nijeriya baya ga Legas. Jihar tana samun kama-baya kowacce rana.
“A baya, ‘yan kasuwa su na zuwa daga jihohin makwafta da ma kasashen waje domin yin sayayya a Jihar Kano, amma wannan lamarin na fuskantar tangarda.
“Manyan ‘yan kasuwan daga Nijar, Kamaru, Chadi da wasu sun maida Kano kamar gidansu. Amma a yau dukkaninsu sun canza. Sayan kayanmu ya ragu.
“Akwai damarmakin ayyukan yi sosai a Jihar Kano kuma akwai kamfanoni da daman gaske wadanda suke taimaka wa rayuwar al’umman. Sai dai a yanzu wasu sun zama tarihi. Wannan matsalar ya sanya matasa sun shiga harkokin shaye-shaye, garkuwa da mutane da fashin daji. Mutane su na rayuwa cikin tsananin ta-lauci, yayin da wasu ko mudun shinkafa ba su iya saye domin iyalansu su ci.
“Zan nemi ganin Shugaban kasa Bola Tinubu na shaida masa irin yunwar da ke addabar al’ummar Kano. Dole gwamnatin tarayya ta bayar da muhimmin tallafi ga jihar da ke da mutane masu tarin yawa.”
Wasu da suka yi magana a madadin ‘yan kasuwan kamar Alhaji Sabiu Bako, Alhaji Salisu Sambajo, Muhammad Adakawa, da Sammani Elsamad, gami da saura sun yi kira ga gwamna Yusuf da ya jagoranci sauran gwamnonin shiyyar arewa maso yamma domin nemo hanyoyin shawo kan matsalolin tattalin arziki da ke addabar al’ummar shiyyar.