A ranar Talata ne mazauna unguwar Sobi Poly da ke Oke-Fomo a karamar hukumar Ilorin ta Yamma, da suka kunshi al’ummomi 44, suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da matsalar wutar lantarki a yankinsu.
Al’ummomin sun kasance cikin rashin wutar lantarki tun watan Fabrairun 2024 (shekara guda).
- Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna
- Gasar Gajerun Labarun Soyayya Ta LEADERSHIP HAUSA 2025
Al’ummomin a yayin zanga-zangar, sun ce karo na karshe da suka ga wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan, IBEDC, ya kawo shi ne a watan Janairun 2024.
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.