Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 don tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, Jihar Borno.
Yayin ziyararsa zuwa babban birnin jihar, Atiku ya bayyana juyayinsa ga Gwamna Babagana Zulum da waɗanda ibtila’in ya shafa, wanda ya raba kimanin mutum 500,000 da muhallansu.
- Rikicin PDP: Daraktan Yakin Neman Zaben Atiku Ya Caccaki Wike
- Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 40 A Hatsarin Kwale-kwale
Atiku ya jaddada ƙudirinsa na tallafawa al’umma, tare da tunatar da irin wannan tallafi da ya bayar a lokacin annobar COVID-19.
Haka zalika, ya bukaci abokansa da hadiman sa da su ba da tasu gudunmawar wajen tallafawa ƙoƙarin rage raɗaɗin bala’in.
A nasa bangaren, Gwamna Zulum ya nuna godiyarsa ga wannan tallafi, tare da yabawa irin haɗin kai da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna.