Sakamakon ruwan sama da aka tafka kamar da bakin ƙwarya a jihar Kebbi jiya Asabar zuwa Wwyewar safiyar Lahadi sama da gidaje 200 sun rushe a masarautar Argungu da ke a jihar.
Saboda irin ruwan sama da aka tafka mai yawa a jihar ta Kebbi inda a masarautar Argungu wasu garuru suka samu asarar gidaje da kuma kayyakin na Miliyoyin Nairori a garin Bayawa, da Tiggi, da fakon Sarki da bakin KARDA shigo wa garin Argungu. Inda gidaje fiye da Dari biyu saka rushe.
- Zanga-zanga: Kebbi Ta Bukaci Matasa Da Su Guji Tashe-tashen Hankula
- Gwamnatin Kebbi Ta Ƙaddamar Rabon Taki Ga Manoma 48,000 Kyauta
A halin yanzu dai mutanen garin Bayawa na zaune ne a cikin Makarantar sakandare ta garin na Bayawa a matsayin matsugunni na wuccin gadi. Haka kuma mutanen garin fakon Sarki na zaune ne Makarantar Magajin Rafi da ke sabon garin bariki a cikin garin na Argungu a matsayin wata mafaka ta wuccin gadi. Har ila yau garin Tiggi sun koma cikin Makarantar sakandare da ke garin na Tiggi don samun wajen kwanciya.
Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida ya yi tattaki zuwa waɗannan garuruwan don ganin irin yadda ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da kuma jajantawa ga jama’ar waɗanda garuruwan da abin ya shafa. Inda anan take ya ba da umurnin ɗaukar sunayen dukkan mutanen da ambaliyar ruwan ta lalata wa gida da kuma irin dukiyoyin da aka yi asara.
Kazalika, Mataimakin Gwamnan dai, ya umurci Shugabanni ƙananan Hukumomin biyu na Argungu da Augie da su gaggauta kwashe mutane zuwa makarantun boko da ke kusa da su don samun wajen kwanciya na wuccin gadi kafin sama musu tallafi na gaggawa.
Acewar, daya daga cikin wanda abin ya shafa wanda ya nemi a sakaye sunansa da ke a garin Bayawa ya ce “A jiya Asabar ne aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya har ruwan ya rushe mana gidajenmu. Amma babu salwanta rayuwa, mun rasa gidaje da sauran wasu dukiyoyin mu”, Inji shi.