Uwargidan Gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Hafsa Kollere Buni, ta jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno bisa ibtila’in ambaliyar ruwan da ta same su.
A wata sanarwar da ta fitar ga manema labarai, uwargidan gwamnan ta ce, “Zuciyata tana tare da ‘yar ‘uwata Uwargidan Gwamnan Borno, da mutanen Jihar Borno masu kwazo da juriya a wannan lokaci na jimami sanadiyyar ambaliyar ruwa mafi muni da ta faru a birninmu na Maiduguri mai albarka.
- Shugaba Xi Ya Ba Da Umarnin Karrama Wasu Mutane 15
- Sin Na Shirin Soke Daukacin Haraji Kan Hajojin Dake Shiga Kasar Daga Kasashe Mafiya Karancin Wadata
“Rashe-rashen da aka yi, da asarar dukiya, abin bakin ciki ne kwarai. A matsayinmu na ‘yan uwa, muna tare da ku a cikin wannan juyayi, kuma muna taya ku da addu’a. Allah Ya karfafa zukatanmu don yin nasara wajen farfaɗowa daga wannan asara da aka yi.
“Hakika, tare za mu tsallake wannan jarabawa, tare da duk wadanda da abin ya shafa. Kuma ina kira da a karbi wannan kaddara cikin kwarin gwiwa.” In ji sanarwar.