Mataimakiyar Shugaban Asusun bunkasa noma na kasa da kasa Katherine Meighan ta bayyana cewa, asusun ya taimaka wa wasu manoma a kasar nan da dala miliyan biyar.
Meighan ta ce, asusun ya bayar da kudin ne ga gwamnatin kasar domin a tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gonarsu.
Mataimakiyar ta bayyana hakan ne lokacin wata ganawa ta musamamn da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mohmood Abubakar a Abuja wadda ta ce, asusun ya bayar da taimakon ne don tausaya wa manoman da iftila’in na ambaliyar ruwan ta shafa.
“Mun bayar da kudin ne ga gwamnatin kasar domin a tallafa wa manoman da ambaliyar ruwa ta lalata gonakinsu”.
Meighan ta jinjina wa gwamnatin kasar bisa zuba jarin da ta yi a harkar noma, musaman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma ci gaba da habaka fannin aikin nama a Nijeriya.
“A susun na kuma yin aikin kafada da kafada da gwamnatin kasar nan, musamman kan yadda za a mayar da hankali matuka a kan kananan manoman da ke a cikin karkara”.
Ta kuma nuna jin dadinta bisa karin tallafin, musaman domin a kara habaka fannin aikin noma a fadin kasar nan, inda ta kara da cewa, asusun na kuma yin aikin kafada da kafada gwamnatin kasar nan, musamman kan yadda za a mayar da hankali matuka a kan kananan manoman da ke karkara.
A na sa jawabin ministan ya mika godiyasa a madadin gwamnatin tarayya a kan wannan tallafin kudaden, inda ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatin za ta tabatar tallafin ya kai ga wadanda aka yi abin dominsu.
A wani labarain makamancin wannan kuwa, rahotannin da suka fito daga wasu jihohin kasar nan sun ce, iftila’in na ambaliyar ruwa ta kara janyo hauhawan farashin shinkafa da sauran amfanin gona.
An ruwaito wasu daga cikin manoman shugabanin kungiyar manoman masara sun sanar da cewa, mai yuwa farashin ya karu rashi, saboda da tsadar takin zamani da manoma suka fuskanta a daminar bana, inda suka yi kira ga sauran takwarorinsu kan su guje wa sayar da amfanin gonakarsu bana domin gudun kauwace wa faskantar matsala.
Sun yi nuni da cewa, akwai matukar bukatar, gwamnatocin kasar nan, musamman gwamnatin tarayya da kawo masu dauki, musamman domin kar su durkushe a cikin fannin.
An ruwaito cewa, a yanzu haka dai a wasu kasuwannin da ke a kasar nan, musaman a jihar kaduna, buhun shinkafa mai nauyin kilo 100 ana sayar da shi naira 19,000 21,000.
Sai dai, kuma, farashin buhun waken soya ana sayar da shi kan naira 22,000 zuwa naira 24,000, inda buhun masara ya kai nira 16,000, kuma buhun farin wake, ana samun sa a kan 44,000 saboda ba a shiga kakarsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp