Dubban mutane sun fara bari gidajensu a Maiduguri da ke Jihar Borno, sakamakon ambaliyar ruwa da aka tashi da ita a garin.
Masana sun yi gargain sake yiwuwar tsanantar ambaliyar a kownne lokaci daga yanzu.
- Babu Bukatar Tada Hankali Kan Karuwar Farashin Mai – IPMAN Ga ‘Yan Nijeriya
- Shugaban Zimbabwe: Zimbabwe Da Sin Na Da Matsaya Daya A Gaban Kalubaloli
Rahotanni sun ce galibin yankunan da ambaliyar tafi tsananta na a karamar hukumar Jere, ambaliyar da aka fara gani tun mako guda da ya gabata amma kuma ta tsananta a safiyar yau.
Lamarin ya sanya gwamnatin jihar kulle makarantu sakamakon gargadi da masana suka yi na ta’azzarar ambaliyar.
Wasu mazauna birnin sun bayyana cewa yanzu haka ambaliyar ta tilasta kwashe al’ummomin Fori da Galtimari da Gwange da kuma Bulabulin sakamakon yadda ruwa ya shanye muhallansu.
Tuni wasu bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta suka nuna yadda motoci ba su iya motsawa a wasu sassa na Maiduguri sakamakon yadda tituna suka shafe da ruwa.
Tuni mazauna birnin suka nemi daukacin al’ummar Musulmi su taya su da addu’a.