Akalla mutane 50 ne suka mutu yayin da da dama suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa.
Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na Jihar (SEMA), Sani Yusuf, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Lahadi.
- ‘Yansanda Sun kama Wani Babban Dan Damfara A Legas
- Za A Dawo Da Shingen Binciken ‘Yansanda A Fadin Nijeriya
Ya bayyana cewa ambaliyar ta kuma lalata dubban gidaje, inda ya kara da cewa hakan ya tilastawa mazauna garin da dama neman mafaka a gine-ginen gwamnati.
Ya ce gwamnatin jihar ta bude sansanonin wucin gadi 11 ga mutanen da suka rasa matsugunansu.
A cewarsa, wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun fito ne daga kauyen Balangu, inda gidaje akalla 237 suka nutse tare da kashe mutane hudu.
“Muna da ‘yan gudun hijira da yawa a sansanonin wucin gadi 11. A Balangu kadai gidaje 237 ne suka lalace kuma mutanen da ke zaune a sansanin na wucin gadi ne,” yayin da bayyana.
Tun bayan da damina ta fara kankama Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasa (NiMET), ta gargadi jama’a da su zama masu kula saboda mamakon ruwa da za a samu a bana.