Shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya, reshen karamar hukumar Sabon Gari, Alhaji Yahuza Suleiman dan Sa’a ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fitar da wasu tsare-tsare da za a tallafa wa manoman shinkafa da suka sami matsalar sakamakon ambaliyar ruwa a gonakinsu a wannan shekara.
dan Sa’a ya yi wannan kira ne a lokacin da ya zanta da wakilinmu da ke Zariya, kan matsalolin ambaliyar ruwa da manoman shinkafa suka tafka asara a gonakinsu a damunar bana.
- Rahoto: Kasar Sin Ta Kara Saurin Inganta Bangaren Makamashi Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Cikin Shekaru Goma Da Suka Gabata
- Ina Da Kishin Bunkasa Rayuwar Mata Da Kananan Yara Tun Ina Karama – Fatima Dala
Ya kara da cewa mafiya yawan manoman shinkafa a kananan hukumomin Jihar Kaduna sun tafka asarar da babu wanda ya isa ya bayyana yawan asarar da aka yi, sai dai a kimanta kawai.
Ya tabbatar da cewa sun yi nisa wajen tantance asarar da manoman shinkafar suka yi a gonaknsu, sai dai kuma nan gaba kadan za a iya tattance wadanda suka tafka sarara a gonakisu.
Ya kuma shawarci gwamnatin tarayya ta fara tunanin tallafin da za ta ba wadanda suka yi asarar, ba a bar su haka kawai ba, in haka ya tabbata za su sami mafita daga asarar da suka tafka a dalilin wannan ambaliya da ta faru.
Ambaliyar Ruwa: Ya Dace Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Shinkafa – dan Sa’a
Shugaban kungiyar manoman shinkafa na Nijeriya, reshen karamar hukumar Sabon Gari, Alhaji Yahuza Suleiman dan Sa’a ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fitar da wasu tsare tsare da za a tallafa wa manoman shinkafa da suka sami matsalar sakamakon ambaliyar ruwa a gonakinsu a wannan shekara.