Shugaban kungiyar Fityanul Islam ta kasa Sheikh Muhammad Arabi Ahmad Abul -Fatahi, ya bayyana cewa amfani da bindiga kadai ba zai magance matsalar tsaron da yayiwa Arewacin Kasar nan katutu mafita ba.
Ya ce.” Bindiga Baza kawo mafita wajen warware matsalar rashin tsaro a Arewa ba har sai mun koma ga koyarwar Annibi Muhammadu (SAW) mu gyara halayenmu wajen tsarkake zukatanmu, kamin zamu iya samun mafita”
- Muna Bin ‘Yan Bindiga Har Maboyarsu Mu Fatattake Su – Minista
- Gwamnatin Kano Da ICPC Sun Kulla Alakar Aiki Kan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa
Shugaban ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu jim kadan bayan bude taron majalisar koli na kungiyar fityanu wanda aka gudanar da shi a dakin taro na jami’ar jihar Kaduna.
“Matsalar tsaro a Arewa Abune wanda ba boyayyan Abu bane Abu ne wanda kowa yasan halin da Arewacin Nijeriya take ciki musamman a bangaren tsaro muna cikin Hali mawuyaci idan bamuyi hankali ba mu da kanmu zamu war wargaza jihohinmu ko kanmu saboda mafiya yawanmu musulmi ne domin idan kace kashi 80 cikin 100 na Arewacin Nijeriya musulmi ne baka yi laifi ba.
“Mafita shi ne a koma ga Allah Sai halayen al’umma su gyaru, ba zan manta ba a shekarun baya a Arewa lokacin muna matasa a lokacin Ba’a rufe gidajenmu da dare har abinci ake ajiyawa saboda baki, idan bako ya shigo ba Sai ya nemi abinci ba Amma yanzu abin ba haka yake ba”
Hakazalika, Shehin Malamin ya ce Talauci da rashin aikinyi sune dalilan rashin tsaron.
Sheikh Muhammad Arabi yace Al’umma Suna cikin mawuyacin haii na rashin tsaro da rayuwar kunci inda ya bayyana yunwa da talauci sune silar sace -sace da muyagun ayyuka a Nijeriya.
“Muna kira ga kungiyar gwamnonin Nijeriya da su tabbatar da cewa sun ceto rayuwar al’ummar su saboda ‘Yan Nijeriya suna cikin kuncin rayuwa da rashin zaman lafiya”
Ya kara da cewa ” Muna kira ga Gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa ta sauke nauyin da ta daukarwa al’ummarta kamin zabe”
Da yake bayani akan iftila’in tashin Bam na Tudun Biri , shugaban ya bayyana gansuwarsa da irin matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka yayin faruwar lamarin na Bawa mutanan gudummawar gaggawa.
A kan Hakan ya bukaci gwamnatin tarayya Data tabbatar da ta hukunta wadanda suka kai harin tare da cika alkawarin da gwamnati ta daukarwa al’ummar kasar na kare rayuka da dukiyar al’ummar kasar baki daya.
A jawabin Shugaban Taron Sanata Abu Ibrahim, yace ya zama wajibi al’umma su dage da addu’a domin samun zaman lafiya a Nijeriya.
Ya ce Babu wata gwamnatin da zata goyi Bayan sace -sace da rashin zaman lafiya.
Abu Ibrahim, wanda Sanata Mukhtar Mohammed Dan Dutse ya wakilta, ya taya kungiyar Fityanul Islam murnar cika shekara 60 da kafuwa.
Ya ce “Ganin yadda kungiyar ta dade tana bayar da gudummawa wajen tallafawa addinin musulunci, akwai bukatar a samar da jami’ar musulunci mallakin Fityanul”