Babu shakka, itacen Aduwa sanannen abu ne a kasar Hausawa, musamman a yankunan karkara, har ma da biranen. Ana tsotsar ‘ya’yan aduwa ko kuma shan su.
Har ila yau, ana amfani da Mai da ‘ya’yan Aduwa; wajen yin magunguna da dama. Kazalika, itacen Aduwa na fid da kwallaye masu matukar amfani a jikin mutum, ta hanyar sarrafa magunguna daban-daban.
- Yadda Bankuna Da Cibiyoyin Kudi Ke Tafka Asara Sakamakon Fara Amfani Da Fasahar Zamani Ta AI
- Musabbabin Faduwar Farashin Tumatir Warwas A Legas Da Sauran Wasu Jihohi
Aduwa ta yi matukar suna a kasar Hausa, musamman a yankunan karkara. Su dai, wadannan ‘ya’yan Aduwa ana tsotsar su ne ko kuma a sha. Bayan sha da ake yi kuma, a kan tatsi Mai daga kwallon na Aduwa.
Ana kiran Aduwa a turance da ‘Desert Date’. Sannan, bincike ya nuna cewa, ana tatsar Man da ke cikin kwallon ‘ya’yanta, sannan kuma; shi kansa itacen nata na da matukar muhimmanci, wajen samar da magunguna na cututtuka daban-daban.
Ga Wasu Daga Cikin Amfanin Aduwa A Jikin dan’adam Kamar Haka:
1- Aduwa na kawar da cutar asma, ta rabu da mutum har abada.
2- Mai fama da atini ko zawo, zai samu sauki nan take; ta hanyar tsotsan wannan Aduwa.
3- Aduwa na kawar da tsutsar ciki.
4- Sannan, tana maganin ciwon shawara.
5- Aduwa na maganin fyarfyadiya, ga masu fama da wannan cuta.
6- Man kwallon Aduwa, na rage kiba a jikin mutum, idan ana girka abinci da shi, ma’ana yana narkar da kitsen da ke taruwa a jikin dan’adam.
7- Kazalika, yana warkar da ciwo a jiki; musamman idan ciwon ya zama gyambo.
8- Man Aduwa, na maganin sanyin kashi da kuraje.
9- Yana kawar da kumburi kowane iri a jikin mutum.
10- Kana yana kawar da matsalar yin fitsari da jini.
11- Man Aduwa, na gyara fatar mutum tare da hana shi saurin tsufa.
12- Sannan, yana kuma kawar da ciwon buguwa; ma’ana idan mutum ya buge a hannu ko kafa ko kuma wani sassa daga jikinsa.
Allah yasa mu dace, amin