5- Ana amfani da hulba wajen maganin cushewar ciki: Hulba na taimakawa wajen saurin narkewar abinci, sakamakon haka ake yin maganin cushewar ciki da ita. Duk masu fama da matsalar cushewar ciki ko kumburin ciki, sakamakon rashin narkewar abinci; sai ya jibanci amfani da hulba, zai samu afuwa da yardar Allah.
6- Mata na amfani da hulba don samun karin ni’ima: Idan mace na fama da rashin ni’ima ko bushewar gaba, za ta iya samun hulba ta yi amfani da ita.
Yadda za ta yi amfani da hulbar; don samun karin ni’imar shi ne, sai ta samu ‘ya’yan hulba, kanumfari, ‘ya’yan habbatus-sauda da kuma Zumarta mai kyau.
Sai ta hada ‘ya’yan hulbar da na habbatus sauda da kanumfari waje guda ta dafa su, bayan sun dahu sai ta sauke ta jira ya huce, sannan sai ta zuba zuma a ciki; ta rika sha, za ta sha mamaki da izinin Allah.
7- Hulba na taimakawa wajen rage kiba ko teba; kamar yadda muka ambata a sama, mutanen nahiyar Asia na amfani da hulba a kan matsalolin lafiya da dama, haka nan game da matsalar kiba ma, sukan yi amfani da hulba; don samun waraka. Yadda suke yi kuwa shi ne, yawan sanya ta a cikin cimarsu.
8- Amfani da hulba na kara inganta lafiyar koda: Masana sun tabbatar da cewa, yawan amfani da hulba a cikin abinci na kara inganta lafiyar koda, ta hanyar sabunta kwayoyin halittar kodar tare da hana su lalacewa.
9- Hulba na kare hanta daga kamuwa da cututtuka: Yawan amfani da hulba na taimakawa wajen kare hanta daga kamuwa da cututtuka. Masana sun ce, hulba na yin wannan aiki ne ta hanyar fitar da sinadarai masu guba da ka iya yin lahani ga hanta.
10- Amfani da hulba na taimaka wa masu fama da ciwon siga: An gano cewa, amfani da hulba na taimaka wa masu fama da larurar ciwon siga. Masana sun ce, hulba na wannan aiki ne, ta hanyar daidaita sigan da ke cikin jini.
11- Hulba na taimakawa wajen sha’awar cin abinci: Ana amfani da hulba wajen magance matsalar rashin cin abinci. Idan mutum na fama da rashin sha’awar cin abinci, sai ya samu man hulba ya hada da zuma ya rika shan babban cokali biyu; sau uku a rana.
12- Ana amfani da hulba don karin kiba: Mai karatu ba zai yi mamaki da ganin wannan ba, musamman idan ya yi la’akari da yadda muka bayyana a sama cewa, hulba na taimakawa wajen sha’awar cin abinci, mun san kuwa cin abinci na da kyakkyawar alaka da samun kibar jiki. Saboda haka, mutanen da ke fama da matsalar rama, sakamakon murmurewa daga wata rashin lafiya za su iya amfani da hulba, don samun waraka. Kazalika, za su iya amfani da hadin da muka fada a sama, a kan karin cin abinci; domin wannan fa’ida.
Sai dai, wani tsokaci a nan shi ne, duk mai son yin amfani da hulba don karin kiba, akwai bukatar bayan amfani da hulbar ya hada da cin abinci mai gina jiki, kamar wake, dankalin turawa, kifi da sauransu, domin kuwa Hausawa na cewa; “ko da kana da kyau ka kara da wanka”, kuma ko babu komai wadannan dangin abinci za su taimaka maka wajen kara wa jikinka karfi. Haka zalika kuma, sai ka guji cin nau’ikan abinci masu maiko sosai.
13- Hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon daji: Babu shakka, hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon dajin mama, musamman ga mata masu shayarwa. Bincike ya nuna cewa, matukar mace mai shayarwa ta juri amfani da hulba, baya ga kara mata lafiya tare da jaririnta, zai kuma ba ta kariyar kamuwa da ciwon dajin mama (Breast cancer).
A kwai ci gaba