Lalle na cikin wani sinadarin da ke dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mu yi lalle akwai sirrika a cikinsa.
Amfanin Lalle Don gyaran Fata:
Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata, domin shi ‘natural toner’ ne wanda ba bilicin yake yi ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.
A bangaren gyaran fuska, yana sa fuska tai kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan kwai amma banda kwaiduwar kwan.
ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum 30 mins kafin wanka sai kinga bambanci a cikin sati biyu Insha Allahu
Ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafawa a fuskar ki bayan watanni kuraje za su mutu sannan tabo ba zai zauna ba ga hasken fuska da laushi.
Sannan ga Amare Kafin ki yi dilke na aurenki ki kwaba lalle mai kyau tare da turare mai maiko, turaren gargajiya mai mai, ki jika kamar bucket daya kada yayi ruwa ruwa sosai kamar dai kunu, kullum sai ki shafa a dukkan jikinki sai ki zo ki saka turaren wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara jikinki har sai hayakin turaren nan ya shiga jikinki sosai sai ki fita kije kiyi wankan ki,za kiga canji a fatar ki rapid canji kuwa. Fata za ta yi laushi, haske da kuma santsi. Two months before bikin ki zaki iya wannan kedakanki kuma zaki ji dadi.
Lalle nasa cikan gashi, ba yasa gashin kan mace ya zube, yana da matukan amfani wajen gyara gashin mace, inda wasu ke tura (steaming) gashin su dashi ma’ana.