ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Man Kade A Gyaran Fatar Jikin Mace

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Man kade

Kadanya wata bishiya ce da ta ke samar da ‘ya’ya koraye ma su zaki. Kwarai kuwa ‘ya’yan kadanya korra ne ko da sun nuna. Daga ‘ya’yan ne ake samar da man kadanya bayan an sarrafa su.

Wasu mutanen na kiran sa man kade, yayin da wasu ke kiran sa da man kadanya. Ko da wanne suna ka san shi, ba shakka man kadanya na da matukar amfani wajen inganta lafiyar dan-adam.

Tun zamani mai tsawo da ya shude ake amfani da man kadanya wajen samar da magungunan kan wasu matsalolin lafiya musamman matsalolin da su ka shafi fata saboda man kadanya na kunshe da sinadarai da dama da su ka hada da sanadaran Bitamin A, Bitamin E, Calcium da sauran su.

ADVERTISEMENT

Daga cikin amfanin man kadanya, akwai maganin kurajen fuska da sanya laushin fata da maganin kyasbi, hakanan ana amfani da man kadanya wajen maganin fason kafa da bushewar fata, da dai sauran amfani da man kadanya ke samar wa dan adam.

Ba tare da bata lokaci ba, za mu kawo wasu daga cikin amfanin man kadanya wajen inganta lafiyarmu.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za Ku Gyara Kanku

Maganin Nankarwa (4)

  1. Amfanin man kadanya wajen maganin fason kafa; Ana amfani da man kadanya sabuda maganin fason kafa. Don samun wannan amfani na man kadanya, mutum zai yi takidin mansa mai kyau, idan dare ya yi kafin ya kwanta, sai ya goge kafarsa sannan ya shafe ta da man kadanya, sai ya sanya kafar cikin leda sannan ya sanya cikin safa, idan gari ya waye sai ya cire ya wanke. Haka zai juri yi musamman idan a lokacin hunturu ne, da sannu zai ga abin mamaki.
  2. Man kadanya na maganin kyasbi; Hakanan ana amfani da man kadanya don maganin kyasbi. Idan mutum zai hada maganin kyasbi da man kadanya, sai ya samu man sandal da man ‘labender’ ya zuba cikin man kadanya sannan ya kwaba sosai sannan ya samu mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya zuba wannan hadin ya adana.
    Yadda zai yi amfani da shi, shine, ya mayar da wannan hadin manmnyka tamkar man shafawasa, ma’ana zai ke yin amfani da wannan hadin a kullum har tsawon watanni shida. Idan Allah Ya so za a dace.
  3. Ana amfani da man kadanya don laushin fata; Ga wanda ya ke son fatarsa ta kasance mai laushi, shin mace ce ko namiji sai ya yawaita shafa man kadanya a duk ilahirin jikinsa bayan ya/ta yi wanka. Ba shakka yin hakan na sanya laushin fata.
  4.  Man kadanya na rigafika wasu cutukan fata; An samu sahihin bayani game da yadda man kadanya ke yin riga-kafin wasu cutukan fata. Idan mutum na yawan amfani da man kadanya zai samu kariya daga kamuwa daga wasu cutukan fata. Idan ya so zai yi amfani da man kadanya kamar yadda mu ka ambata a lamba ta 3 da ke sama.
  5. Man kadanya na maganin gautsin fata; Wasu mutanen Allah Ya jarrabe su da gautsin fata. Da zarar fatarsu ta sha wahala ba wuya ta samu lahani, to ma su fama da irin wannan matsala ta gautsin fata na iya amfani da man kadanya don samun waraka.
    Duk mai fama da wannan matsala ya samu man kwakwa da man zaitun da kuma man ‘almond’ ya hada su ukun da man kadanya ya kwaba su, ya tabbatar sun kwabu sosai, sai ya zuba a cikin mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya adana. Wannan hadin zai rika shafawa a dukkan jikinsa. Don samun cikakkiyar fa’ida sai ya mayar da man kadanya matsayin man shafawarsa kowanne lokacin idan ya fito daga wa
  6. Man kadanya na maganin bushewar labe; A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kadanya a kwaba sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi . Sai a rika shafawa a labban baki a kullum za a samu sauki.
  7. Ana amfani da man kadanya don gyaran gashi; yawaita Kitso da man kadanya na magance wasu cutukan fatar kai kamar, makero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za Ku Gyara Kanku
Ado Da Kwalliya

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025
Maganin Nankarwa (4)
Ado Da Kwalliya

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Next Post
Kungiya Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Watsi Da Kashin Kajin Da Ake Shirin Lika Wa Shugaban NNPC

Kungiya Ta Bukaci Tinubu Ya Yi Watsi Da Kashin Kajin Da Ake Shirin Lika Wa Shugaban NNPC

LABARAI MASU NASABA

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025
ECOWAS

A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS

November 16, 2025
APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe

November 16, 2025
Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya

November 16, 2025
Kwankwaso

NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji

November 16, 2025
Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?

November 16, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

November 15, 2025
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.