Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce, amincewa da yarjejeniyar dakile bazuwar bindigogi, muhimman mataki ne da Sin ta dauka, don ingiza manufar tsaron duniya baki daya.
Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Larabar nan, ya ce matakin na Sin zai ingiza cudanyar sassa daban daban, da wanzar da zaman lafiya da daidaito tsakanin sassan kasa da kasa.
Rahotanni na cewa, a jiya Talata ne wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya mika takardun amincewar Sin da yarjejeniyar ga babban magatakardar MDD Antonio Guterres. Kaza lika ra’ayoyin al’umma na nuna cewa, amincewar Sin da yarjejeniyar dakile bazuwar bindigogi za ta taimakawa Sin din, da sauran kasashe masu tasowa, cimma nasarar hadin gwiwarsu, a fannin yaki da bazuwar bindigogi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)