A martaninta dangane da furucin sakataren wajen Amurka Anthony Blinken game da jihar Xinjiang ta Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning, ta ce Amurka na yin biris da gaskiya, tana sukar manufofin addini na kasar Sin, wanda cike yake da son zuciya, kuma tsoma baki ne cikin harkokin gidan Sin.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Juma’a, tana mai cewa, Sin na adawa da matakin na Amurka.
Game da batun bashin Sri Lanka kuwa, Mao Ning ta ce Sin ta tsawaita lokacin biyan bashin a shekarar 2022 da kuma ta 2023, domin taimakawa kasar rage matsin biyan bashi na gajeren lokaci.
Har ila yau, yayin da ake cika shekara 1 da bude wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, Mao Ning ta ce Sin za ta ci gaba da amfani da gogewar da ta samu daga wasannin da karfafa musaya da hadin gwiwa da dukkan bangarori da bayar da gagarumar gudunmuwa ga raya harkar wasannin Olympics. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)