Sojojin Korea ta Kudu da na Amurka sun har ba wani makami mai linzami a cikin teku wanda ke matsayin mayar da martani ga Korea ta Arewa da ta har bana ta makami mai linzamin da ya ratsa sararin samaniyar kasar Japan.
Atisayen hadin gwiwar tsakanin Sojin Korea ta Kudu da na Amurka, na zuwa ne a dai-dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke shirin wani zama na musamman don tattaunawa kan abin da Korea ta Arewan ta aikata ga Japan.
- Samar Da Ingantattun Bayanan Kidaya Sirri Ne Na Kyakkyawan Ci Gaba – Ganduje
- Yadda Mamu Ya Dinga Kawo Cikas Ga Ceto Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna – Atta
Majiyoyi daga bangaren Amurka da Korea ta Kudu sun tabbatar da gwaji na ranar Laraba wanda suka harba makamin cikin tekun Yellow Sea kuma ya ci tazara mai tarin yawa.
Sai dai wata majiya daban ta bayyana yadda wani gwajin makami da sojin Korea ta Kudun suka gudanar duk dai a yau din ya yi rashin nasara bayan da ya dawo jim kadan bayan harba shi sararin samaniya ko da ya ke babu wanda ya samu rauni.
Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuno yadda hayaki ke tashi da tartsatsin wuta a wajen da sojojin na Amurka da na Korea ta Kudun suka gudanar da gwajin.
Har zuwa yanzu dai Korea ba ta ce uffan game da gwajin na ta da ta harba makamin mai cin matsakaicin zango tasararin samaniyar Japan ba.
Gwajin na Korea ta Arewa, shi ne karon farko cikin shekaru biyar da ta harba makamin da ya ratsa sararin samaniyar Japan, lamarin da ya sa gwamnatin Japan din bai wa mutane umarnin neman mafaka a ranar Talata, baya ga kunna na ta makaman masu linzami saboda kariya daga yiwuwar fuskantar farmaki.