• English
  • Business News
Sunday, November 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka, Ki Fahimci Cewa “Girma Da Arziki Ke Sa A Ja Bajimin Sa Da Zaren Abawa”

by CGTN Hausa and Sulaiman
7 months ago
Amurka

Matakan karbar karin haraji kan kayayyakin ketare da kasar Amurka ta dauka na ci gaba da haifar da barazana ga kasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya.

Jiya, Jaridar Premium Times ta wallafa wani bayani na Victor Liman, tsohon wakilin Najeriya mai kula da shawarwari kan batun cinikayya, wanda ya yi tsokaci kan tasirin da matakan kasar Amurka za su iya haifar wa Najeriya. A cewar mista Liman, matsalolin da Najeriya za ta iya fuskanta sakamakon matakan kasar Amurka sun hada da gibin kasafin kudi, da hauhawar farashin kayayyaki, da rashin jarin da ake zubawa a kasar, da raguwar guraben aikin yi, da dai sauransu.

  • Kotu Ta Tsare Matasa 2 Kan Wallafa Bidiyon Batsa A TikTok A Kano
  • Kasashen Da Mata Ba Su Taba Mulki Ba A Tarihi

A nata bangare, kasar Sin tuni ta lura da illar da matakan karbar karin haraji na kasar Amurka za su haifar wa kasashe masu tasowa. A wajen hirar da ministan kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao ya yi tare da darekta janar ta kungiyar ciniki ta duniya (WTO) Madam Ngozi Okonjo-Iweala, a kwanan baya, Wang ya ce, matakan kasar Amurka na karbar karin haraji za su iya haifar da mummunar illa, har ma haddasa rikici a bangaren ayyukan jin kai a kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen da ke fama da koma bayan tattalin arziki.

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

Ban da haka, Wang ya ce matakan kasar Amurka sun karya ka’idojin kungiyar WTO na rashin nuna bambanci, da takaita karbar haraji, kana suna girgiza tsarin tattalin arzikin duniya, da tushen tsarin cinikayya da ya shafi bangarori daban daban. Ganin haka ya sa kasar Sin daukar matakan ramuwar gayya kan kasar Amurka, don kare halaltacciyar moriyar kai, gami da neman tabbatar da adalci a duniya.

Da ma shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya gabatar da jerin zafafan matakan tattalin arziki ne don neman daidaita matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta. Sai dai ra’ayinsa na dora “Amurka ta zama gaba da komai” na tarnake masa damar samun biyan bukata.

Raymond Thomas Dalio, shahararren mai kula da sha’anin hada-hadar kudi ne, wanda ya kafa kamfanin Bridgewater Associates, ya tattauna tare da ‘yan jarida a kwanan baya, inda ya fayyace matsalolin da kasar Amurka ke fuskanta a fannin tattalin arziki, kamar su: dimbin bashin da ake binta, da rashin karfin samar da kayayyakin da take bukata, da dai sauransu. A cewarsa, Amurka ta riga ta tsunduma cikin mawuyacin hali na cin bashi da kashe kudi fiye da kima a kai a kai, lamarin da ya haddasa rushewar tsarin kudi da siyasa na duniya, da kawo karshen zamanin tilasta zama karkashin jagorancin kasar Amurka. Kana mista Dalio ya ce yanzu haka, Amurka na neman daidaita matsalolin da take fuskanta ta hanyar ta da rikici a duniya, da karin matsin lamba ga sauran kasashe, lamarin da a cewarsa zai iya haifar da sakamako mafi muni, da kawo tafiyar hawainiya ga tattalin arzikinta.

Hausawa kan ce “Girma da arziki ke sa a ja sa da zaren abawa.” Sai dai a nata bangare, kasar Amurka ta tsaya kan daukar matakan radin kai, da matsawa da cin zarafin sauran kasashe, duk da cewa tana bukatar samun taimako daga saura wajen daidaita matsalar da take fuskanta, inda kuma sam ba zai yiwu ta samu biyan bukata ta wannan turbar ba.

A karshe dai za a lalubo dabara kamar yadda minsta Wang Wentao ya fada, “nemo bakin zaren wareware matsala ta hanyar shawarwari, bisa tushen girmama juna, da zaman daidaito”, matukar ana son warware matsalar.

Muna fatan ganin kasar Amurka ta zama mai sanin ya kamata, da wajabta wa kanta iya sauraron shawara, da daukar mataki mafi dacewa. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Ra'ayi Riga

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Next Post
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Boko Haram Sun Kashe Mutum 300 A Sabbin Hare-hare 252 A Borno – Ndume

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima

November 1, 2025
Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

November 1, 2025
Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

November 1, 2025
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

November 1, 2025
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

November 1, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.