Amurka ta sayi kayayyakin da darajarsu ya kai dala miliyan 643.1 daga Nijeriya a farkon watanni biyu na 2025, wata guda kafin fara aiwatar da dokar haraji ta gwamnatin Shugaba Trump.
Dokokin harajin wanda ta fara aiki daga ranar 9 ga Afrilun 2025, ya sanya masu ruwa da tsaki na nuna damuwa kan irin tasirin da tsare-tsaren harajin za ta iya yi ga kasuwannin Nijeriya.
Ko da yake, an tsame bangare mai da ma’adinai daga sabon tsarin harajin, lamarin da ya dan kawo sauki ga Nijeriya.
Bayanai daga hukumar kasuwancin kasa da kasa ta Amurka na cewa kayan da aka shigo da su daga Nijeriya a watan Fabrairun 2025 ya kai na dala miliyan 286.3, inda ya samu koma-baya ga dala miliyan 423.6 da aka samu a irin wannan lokaci na shekarar da ta gabata.
Jimillar cinikayya tsakanin Amurka da Nijeriya na watanni biyu na farkon shekarar 2025 ya kai kusan dala biliyan 1.33.
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu.
Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.5 cikin dari.
A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari.
Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025, kamar yadda rahoton cinikayyar kayayyaki ta Amurka ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa Amurka ta yi gibin dala miliyan 143 a watan Janairu amma ta samu rarar dala miliyan 187 a watan Fabrairu. Wannan ingantaccen canji ya haifar da rarar dala miliyan 44 a kowace shekara.
Bayanai sun nuna cewa kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa Amurka sun habaka sosai a watan Fabrairu, wanda ya kai dala miliyan 474 idan aka kwatanta da dala miliyan 214 da aka fitar a watan Janairu.
A wani labarin kuma, Ministan Kudi na Nijeriya da Harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce harajin kashi 14 cikin 100 na baya-bayan nan da Amurka ta kakaba kan kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje zai yi wa tattalin arzikin Nijeriya illa.
Edun ya bayyana haka ne a taron kaddamar da harkokin mulki na kamfanoni da ma’aikatar kudi ta kasa ta shirya a Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp