Gwamnatin kasar Amurka da kamfanonin samar da makaman soja na kasar sun kara cin mummunar riba.
A ranar 29 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka ta bayar da sanarwar cewa, a shekarar 2023, kudin makaman soja da ta sayar ga kasashen ketare ya karu da kaso 16%, adadin da ya kai har dalar Amurka biliyan 238. Kafin wannan, alkaluman da cibiyar nazari ta SIPRI da ke birnin Stockholm ta samar sun shaida cewa, daga shekarar 2018 zuwa ta 2022, yawan makaman da kasar Amurka ta fitar zuwa ketare ya dau kaso 40% na dukkanin makaman da aka fitar a fadin duniya, adadin da ya karu da kashi 7% bisa na tsakanin shekarar 2013 da ta 2017.
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Rangadi A Tianjin
- Karuwar Rincabewar Tsaro: Manyan Hafsoshi Sun Shiga Tsaka Mai Wuya
Hakan ya faru ne sakamakon yadda Amurka ta yi ta rura rikici a fadin duniya don cin mummunar riba, matakin da ya lalata zaman lafiya a duniya. Rahoton da cibiyar nazari ta Cato ta kasar Amurka ta fitar ya yi nuni da cewa, daga shekarar 2012 zuwa ta 2022, Amurka ta sayar da manyan makamai da kudinsu ya kai dala biliyan 16 ga kasashe da shiyyoyi 28 da ke fama da rikici a duniya. Bayan barkewar rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, Amurka ba ma kawai ta gaggauta samar da gudummawar soja ga Isra’ila ba, har ma ta sayar da makaman soja ga Isra’ila din har sau biyu a watan Disamban bara, kuma ba tare da an tattauna batun a majalisar dokokin kasar ba. Ban da haka, a bara, Amurka ta ci gaba da rura wutar rikicin Ukraine. Tun bayan barkewar rikicin a watan Faburairun shekarar 2022, Amurka ta riga ta samar da gudummawar da ta zarce dala biliyan 110 ga Ukraine din. A shirin kasafin kudi na bana da gwamnatin Biden ta gabatar, an ware dala biliyan 106 ta fannin samar da gudummawar soja ga Isra’ila da Ukraine da sauransu.
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana a fili cewa, “A hakika kaso 90% na kudin gudummawar soja da muka samarwa Ukraine, an kashe su ne a cikin gidan Amurka, ta fannonin masu samar da kayanmu, kuma hakan ya kara samar da guraben aikin yi ga Amurkawa, tare da sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikinmu.” To, dalili ke nan da ya sa Amurka ke matukar sha’awar tada rikci a duniya.
Ba da jimawa ba bayan barkewar rikicin Ukraine, mista Franklin C. Spinney wanda ya shafe shekaru da dama yana aiki a ofishin ministan tsaron kasar Amurka ya rubuta cewa, rikicin Rasha da Ukraine “ya sa mutane da yawa a ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagon da masana’antun samar da makamai na kasar da ma majalisar dokokin kasar sun taya juna murna asirce. ” Abin haka yake, abin da ke faruwa a kasashen da ke fama da rikici, ba kome ba ne ga ‘yan siyasar kasar Amurka da ma sojoji da masana’antun samar da makamai na kasar, sabo da mummunar riba mai tsoka da suka ci. (Mai Zane:Mustapha Bulama)