Ma’aikatar Lafiya, ta tabbatar da cewa tana shirin karbar kashin farko na rigakafin cutar kyandar biri a mako mai zuwa.
Daraktan kula da cututtuka masu yaduwa da kuma allurar rigakaf, Dakta Garba Ahmed Rufia, ya ce allurar rigakafin guda 10,000 wanda gwamnatin Amurka ta bayar ta hannun hukumarta ta raya kasashe wato USAID, za a yi amfani da su wajen yin rigakafi a jihohi.
- Zulum Ya Raba Wa Magidanta 10,000 Kayan Abinci A Mafa
- Karfafa Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Vietnam
Ya kara da cewa Nijeriya na aiki domin samun karin allurai da za a rarraba.
“Wannan ba shi ne rigakafi na karshe da zai zo kasar nan ba. Muna tsare-tsare wajen tabbatar da cewa karin allurai sun zo, ganin cewa akwai masu bukata da yawa,” in ji shi.
Yanzu dai ana horar da jami’an lafiya domin gane alamomin cutar kyandar biri da kuma ganin an yi rigakafi a kan lokaci.
Ya ce kare jami’an lafiya da kuma al’umma ya zama wajibi, musamman ta hanyar ci gaba da wayar da kan mutane kan yadda za su kare kansu da kuma daukar matakan kariya domin rage yaduwar cutar.