• English
  • Business News
Wednesday, July 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka Za Ta Girbi Abin Da Ta Shuka A Kan Matakin Soke Takardar Bizar Karatu Ga Dalibai Sinawa

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Amurka Za Ta Girbi Abin Da Ta Shuka A Kan Matakin Soke Takardar Bizar Karatu Ga Dalibai Sinawa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

Kasashen duniya na bayyana rashin jin dadi game da sanarwar da sakantaren harkokin wajen kasar Amurka, Marco Antonio Rubio ya gabatar a ran 28 ga watan nan da muke ciki, wadda ta sanar da soke takardar biza ta karatu da kasar ta bai wa dalibai Sinawa. Game da wannan matakin dake yunkurin cimma buri na siyasa da bayyana bambanci, Sin ba za ta yarda ba, kuma za ta dauki matakan da suka wajaba don kiyaye halastaciyyar moriyar dalibanta dake Amurka.

Farfesa a kwalejin koyar da ilmin diflomasiyya na Sin Li Donghai ya ce, Amurka tana kara tsanantar da takara tsakaninta da Sin a halin yanzu, har al’ummar kasar suna fama da jayayyar al’adu. Hakan ya sa, ’yan siyasa kamar Rubio suna yunkurin yin gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, don yin takara da kasar Sin da fakewa da batun dalibanta dake kasar, ta yadda za ta katse huldarta da Sin a bangaren kimiyya da musanyar al’adu da sauran bangarori, abun da zai taimaka wa matakin yin takara da Sin da cimma burin siyasa bisa radin kai.

Ba kasar Sin kadai ba, duk fadin duniya na fama da matsin matakin da gwamantin Amurka ke dauka a wannan karo. Tun daga watan Afrilun da ya gabata, gwamnatin Amurka ta sanar da soke takardar biza ta karatu na dalibai ko masu aikin koyarwa da masu aikin nazari daga kasa da kasa fiye da 529 a jami’o’i 88 na Amurka. An ba da labari cewa, majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta sanar da dakatar daliban ketare ko masu mu’ammalar al’adu daga neman bizar shiga kasar. Amma, kamar kalmomin da shugaban jami’ar Wesleyan Michael S. Roth ya fada, sabanin burin da gwamantin take sa ran cimmawa, za ta girba abin da ta shuka, domin matakin zai lalata moriyar Amurka.

Tarihi na shaida cewa, kasar dake da ainihin karfi ba ta rufe kofarta ko katse huldarta da ketare. Korar daliban ketare ciki har da dalibai Sinawa da katse huldar al’adu tsakaninta da sauran kasashe ba za su ba da ma’ana ba, sai kara lalata sunanta a duniya, da lahanta moriyarta. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Darajar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso Shida Bisa Dari A Afirilu

Next Post

‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba

Related

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

10 hours ago
Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

12 hours ago
An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

12 hours ago
Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%
Daga Birnin Sin

Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

13 hours ago
Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane 
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane 

14 hours ago
Taron Matasan Sin Da Afrika Kan Tsaro Zai Kirkiro Wata Sabuwar Mahanga Ta Magance Matsalolin Tsaro
Daga Birnin Sin

Taron Matasan Sin Da Afrika Kan Tsaro Zai Kirkiro Wata Sabuwar Mahanga Ta Magance Matsalolin Tsaro

15 hours ago
Next Post
‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba

‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba

LABARAI MASU NASABA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Yara 2 Sun Kuɓuta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno

July 16, 2025
Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?

EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari

July 16, 2025
Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9

July 15, 2025
Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

Ƙungiyar Buzaye Ta Yi Wa Nijeriya Ta’aziyyar Rasuwar Muhammadu Buhari

July 15, 2025
VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

VFS Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Yin Biza Zuwa Birtaniya A Kano

July 15, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

Xi Ya Gana Da Shugabannin Tawagogin Kasa Da Kasa Masu Halartar Taron SCO

July 15, 2025
An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

An Gudanar Da Taro Game Da Sana’ar Sarrafa Sinadarai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Beijing

July 15, 2025
Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%

July 15, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 20, Sun Ƙona Gidaje A Ƙauyukan Filato

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 20, Sun Ƙona Gidaje A Ƙauyukan Filato

July 15, 2025
Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane 

Shugaba Xi Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Koli Game Da Aikin Raya Birane 

July 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.