An ɗauke shugaban haramtacciyar ƙungiyar ‘yan Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu daga gidan yarin da ke Abuja zuwa gidan yari a Sakkwato.
Lauyansa Aloy Ejimakor ne, ya bayyana haka a shafinsa X a ranar Jumma’a.
- Sojoji Sun Kama Babban Mai Sayar Da Miyagun Kwayoyi Ga ‘Yan Ta’adda Na Boko Haram
- Yadda Gobara Ta Lashe Kasuwar Katako Ta Gwambe
Ya ce wannan mataki ya jefa sanya ruɗani saboda yanzu Kanu ya yi nesa da iyalinsa, lauyoyinsa, da magoya bayansa.
“MAZI NNAMDI KANU an ɗauke shi daga wajen DSS a Abuja zuwa gidan yari a Sakkwato, yanzu ya yi nesa da lauyoyinsa, iyalinsa, masoyansa da magoya bayansa.”
A ranar Alhamis ne kotu ta same shi da laifukan ta’addanci guda bakwai, wanda Alƙalin kotun mai Shari’a James Omotosho ya yanke masa hukunci.
An yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan laifuka biyar, shekaru 20 a kan laifi ɗaya, da shekaru biyar a kan wani laifin.
Alƙalin ya ce bai yanke masa hukuncin kisa ba, saboda dokokin duniya na sassauta hukuncin kisa.














