Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya baiwa ma’aikatan jihar hutun kwanaki bakwai amma ban da masu gudanar da muhimman ayyuka, sakamakon matsalolin da ake fuskanta na ambaliyar ruwa da ya addabi jihar.
Ya kuma tabbatar da cewa jihar na bukatar tallafin jin kai inda sama da mutane miliyan daya suka rasa matsugunansu a fadin kananan hukumomin Sagbama, Ekeremor, Ijaw ta kudu, Ogbia, Yenagoa, Nembe da Kolokuma Opokuma, kasuwanni duk sun tsaya, an yi asarar dukiyoyi da gonakai.
Gwamna Diri a wani jawabi da ya yi a jihar a safiyar ranar Talata, ya ce ko da yake ambaliyar ruwa, ibtila’i ne da yake sananne a kowanne zamani da yanzu haka, yake addabar wasu Jihohin Tarayya da dama, kusan mutane miliyan daya ne a yankuna sama da 300 a jihar, suka rasa matsugunansu yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu.
Ya ce muhimman ababen more rayuwa kamar asibitoci da tituna da gadoji da makarantu da suka hada da jami’ar Neja Delta ta Amassoma mallakin gwamnati, asibitin koyarwa na jami’ar Neja Delta, Okolobiri, da jami’ar Afrika, Toru-Orua, duk lamarin ya shafe su sosai.