Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayar da miliyan ₦95 ga iyalan maharba 23 da mutanen gari 10 da ‘yan bindiga suka kashe a ƙaramar hukumar Alkaleri.
Rabon ya zo ne bayan harin da ‘yan fashin daji suka kai a dajin Mansur ranar 4 ga Mayu, inda suka kashe maharba da ke sintiri a kan hanyar Madam da ke makwabtaka da jihar Plateau.
- An Cafke Saurayi Bisa Zargin Yi Wa ‘Yar Budurwarsa Fyade A Bauchi
- Gwamnan Bauchi Ya Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Banga A Alkaleri
Gwamnan ya bayyana cewa ya tattauna da mai bayar da shawara kan tsaro Nuhu Ribadu da Sanatan Bauchi ta kudu Shehu Buba Umar don samun ƙarin taimako daga tarayya.
Ya kuma sanar da shirin ɗaukar ‘yan sintiri 2,100 nan ba da jimawa ba, inda za a fara da 300-500 daga yankunan da aka fi kai hari, kuma za a biya su albashi N70,000 a wata.
Iyalan maharba 13 za su karbi miliyan ₦5m kowanne, yayin da na mutanen gari 10 za su karbi miliyan ₦3m kowanne. An kafa kwamitin rarraba kuɗaɗen ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar Alkaleri Hassan Garba Bajama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp