A yau Jumma’a ne aka gudanar da bikin bude atisayen “hadin gwiwa na teku na 2025″ tsakanin Sin da Rasha a tashar jiragen ruwan soja da ke Vladivostok na kasar Rasha.
Za a gudanar da atisayen hadin gwiwa na tekun ne tsakanin Sin da Rasha daga ranar 1 zuwa 5 ga watan Agusta. An sa wa atisayen taken “Kiyaye tsaron muhimman kafofi cikin hadin gwiwa” da “Mayar da martani ga barazanar tsaro a yammacin Fasifik cikin hadin gwiwa.” Jiragen ruwan kasar Sin da na Rasha za su gudanar da atisaye daban-daban a cikin teku da sararin samaniya kusa da Vladivostok, da suka hada da na fannonin ceto jiragen ruwa, dabarun yaki da jiragen ruwa na hadin gwiwa, da kuma tsaron sararin samaniya da kakkabo makamai masu linzami.
Bayan kammala atisayen, kasashen Sin da Rasha za su kuma gudanar da sintiri na hadin gwiwa a ruwan tekun yammacin Fasifik. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp