• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Bude Bikin Baje Kolin Fina-Finan Asiya Karo Na 4 A Najeriya

by CMG Hausa
3 years ago
Asiya

A ranar Litinin 21 ga watan Nuwambar nan ne aka kaddamar da baje kolin fina-finan Asiya karo na 4 a Najeriya. Bikin wanda ofisoshin jakadancin kasashen Asiya 9 da suka hada da Sin, da Iran da Koriya ta kudu, da kuma Najeriya suka yi hadin gwiwar shiryawa, ya gudana ne a cibiyar nune-nunen al’adun kasar Sin dake birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Cikin jawabinsa yayin bude bikin, jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya ce al’adu su ne ruhin kowace kasa, kuma musayar al’adu tamkar musayar zuciyoyi da rayukan al’ummun kasashen duniya ne. Kaza lika fina-finai na nuna yanayi na sassan al’adun al’ummu daban daban.

  • A Dauki Hakikakin Matakai Domin Kyautata Hulda A Tsakanin Sin Da Amurka

Jakada Cui ya ce dandalin baje kolin fina-finai na hadin gwiwar kasashe daban daban, muhimmiyar hanya ce ta gina dandalin fahimtar al’adun juna, da ma yanayin rayuwar al’ummu, kuma hakan zai ci gaba da ba da gudummawa wajen zurfafa fahimtar juna tsakanin al’ummu, da inganta kawancen kasashe.

Ya ce karkashin hakan, za a iya kyautata fahimtar juna, da inganta kawance dake maye gurbin kyamar juna, kana mutane za su kara rayuwa cikin lumana, kuma duniya za ta samu ci gaba cikin yanayin zaman lafiya. Har ila yau, musayar al’adu kyakkyawar manufa ce da duniya ke son cimmawa, kuma hakan shi ne ainihin dalilin shirya bikin na wannan karo.

Daga nan sai jakada Cui ya shawarci mahukuntan Najeriya da su shirya makamancin wannan biki a Sin, domin baiwa Sinawa damar kallon fina finan Najeriya, tare da kara fahimtar kasar, a matsayinta na babbar kasa a nahiyar Afirka. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka
Daga Birnin Sin

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
Next Post
Yadda ISWAP Ta Kai Hari Sansanin Sojoji, Mutane Da Dama Sun Mutu A Jihar Borno

Yadda ISWAP Ta Kai Hari Sansanin Sojoji, Mutane Da Dama Sun Mutu A Jihar Borno

LABARAI MASU NASABA

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

November 8, 2025
NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.