An bude dandalin babban gidan radiyo da talabijin na kasar Sin ko CMG karo na biyu a birnin Shanghai, taron da ya hallara wakilai daga hukumomin kasa da kasa, da cibiyoyin watsa labarai, da kwararru, da kamfanonin kasa da kasa, domin tattauna mahangar sassan game da manufofin zamanantarwa.
Taron wanda aka kaddamar a jiya Alhamis, na da taken “Bude kofa, tafiya tare da kowa, cimma moriya tare: Hada karfi da karfi a turbar zamanantarwa”, ya gudana ne karkashin hadin gwiwar jagorancin CMG, da hukumar gudanarwar birnin Shanghai. Ya kuma samu mahalarta sama da 230, wadanda suka shiga taron ta yanar gizo da kuma ta zahiri.
Mahalarta taron dai sun amince zamanantarwa irin ta Sin, za ta samar da sabbin damammaki na bunkasa ci gaban duniya, tare da ba da gudummawa ga mahangar kasar Sin, a fannin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama.
Kaza lika, mahalartan sun amince cewa, kamata ya yi kafofin watsa labarai na kasa da kasa su sauke nauyin dake wuyansu, tare da karfafa hadin gwiwa wajen ingiza alakar al’ummu, da koyi daga mabanbantan wayewar kai.
Sannan, a yayin taron, an gudanar da wasu kananan ayyuka guda uku, wadanda suka hada da, “Damar samun yin sauye-sauye a duniya”, “Ci gaba mai inganci ta hanyar zamanantarwa ta kasar Sin” da “Nauyin da ya rataya a wuyan kafofin watsa labarai wajen kawo sauyi a Duniya”. Bakin da suka halarci taron sun ba da shawarwari kan yadda kasashen duniya za su karfafa hadin gwiwa da tinkarar kalubale, da yadda cibiyoyin watsa labaru daga kasashe daban-daban za su inganta cudanya tsakanin jama’a da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi. (Masu Fassara: Saminu Alhassan, Ibrahim Yaya)