Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa halin ‘yan siyasa na bai wa sarakuna mamaki.
Mamakin da suke yi wa ‘yan siyasa, a cewarsa shi ne, lokacin da ‘yan siyasa ke yakin nema zabe sai su zo wurinsu, amma da zarar sun samu nasara ba a kara jin duriyarsu sai bayan shekaru hudu. Ya kara da cewa sarakuna na bukatar samun matsayi a tsarin mulki ba wai saboda yukurin kirkiro wani bangare na gwamnati ba ne a cikin kasar nan.
Sarkin Zazzau ya bayyana hakan ne a lokacin da shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon Tajudeen Abbas ya ziyarce shi a fadarsa da ke Zariya ta Jihar Kaduna.
“Ba za a iya bata kwatanta irin gudummuwar da sarakuna suke bayarwa ba, saboda sarakuna suna taka muhimmiyar rawa tun fara mulkin dimokuradiyya har zuwa yau. Na san cewa mafi yawancinku a nan kuna da alaka da sakakuna ko ta kusa ko ta nesa.
“Abin da yake ba mu mamaki shi ne, mutane suna zuwa wurinmu neman tabarraki lokacin zabe, amma da zarar sun samu nasara, ba za su sake dawowa ba sai lokacin zabe kana su kara tuntubarmu. Kafin yanzu, muna mamakin yadda ake yi wa sarakuna haka, amma kuma sun kasa ganewa cewa su sarakuna a ko da yaushe suna nan kan mukaminsu, ko muna raye ko mun mutu. Duk inda mutum ya je sai ya dawo wurinmu.
“Muna jin yadda wasu ‘yan siyasa ke cewa muna son kirkiro wani bangare na gwamnati. Ina magana amadadin sauran sarakuna kamar irinsu Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Shehun Borno da sauran sarakuna. Mun tattauna kan wannan matsala babu adadi.
Mun je Abuja, inda muka gana da tsohon shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai. Mun gabatar da matsayinmu karkashin jagorancin Sarkin Lafiya wanda shi tsohon alkalin kotun koli ne. Mun zayyana matsayinmu, inda muka mika wa tsohon shugaban majalisar dattawa, mun yi mamakin yadda aka yi watsi da kudurin namu.
“Ina magana ne amadadin daukacin sarakunan Arewa. Muna fatan majalisar kasa da duba wannan kurin tare da aiki a kansa da kuma tabbatar ya zama doka.”
Ya kara da cewa babu abin da Masarautar Zazzau za ta iya cewa sai dai godiya ga Allah da ya azurtata.
Ya ce masarautar da kyankyashe shahararrun ‘yan Nijeriya tun daga kan tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo da ministoci da dama da sakatarorin gwamnatin tarayya, yanzu kuma ga shugaban majalisar wakilai.
Da yake jawabi, Rt. Hon Tajudeen Abbas ya sha alwashin cewa majalisa ta 10 za ta karkiri matsayin sarakuna a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan.
Shugaban majalisar wakilai wanda shi dan asalin garin Zariya ne da yake wakiltar mazabar Zariya a zauren majalisa kuma yana da sarauta a cikin masarautar. Ya ce shi da kansa da kuma sauran ‘yan majalisan wakilai sun fahimci muhimmancin sarakuma, sannan za su tabbatar da cewa sun saka su a cikin kundin tsarin mulki.
“Tun shekaru uku da suka gabata na san cewa akwai takardar da majalisar sarakunan kasar nan suka gabatar, inda suka bayyana yadda sarakuna ya kamata su yi aiki a wannan zamani. Muna yi wa Allah godiya da ya kaddara danku ya zama shugaban majalisar wakilai kuma zai sake yin nazari kan matsayin sarakuna.
“Ina mai tabbatar muka cewa ni da suran ‘yan majalisa za mu sake bankado takardar da majalisar sarakuna ta rubuta domin tabbatar da cewa an sama aikin sarakuna a cikin kundin tsarinmulki.
“Za mu yi aiki kafada da kafada da dukkan majalisun kasa domin sake dawo da martabar sarakunan gargajiya.”
Ya nuna jin dadinsa ga sarkin da kuma daukacin mutanen masarautar Zazzau bisa wannan ziyara ta farko tun bayan da ya zama shugaban majalisar wakilai.