An bude dandalin Tunis na bunkasa hadin gwiwar ayyukan likitanci tsakanin Sin da kasashen Afirka. Taron irinsa na farko da aka bude a jiya Juma’a a birnin Tunis na kasar Tunisiya, ya hallara jami’ai, da masana a fannin aikin likita, da kwararru a fannin kiwon lafiya, da wakilan ‘yan kasuwa na Sin da na sassan nahiyar Afirka.
Ma’aikatar lafiya ta kasar Tunisiya, da hukumar kiwon lafiya ta Sin ne suka shirya taron na kwanaki biyu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannin kiwon lafiyar al’umma, da zurfafa musayar kwarewa a bangaren ilimin likitanci tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka.
Cikin sakonsa ta kafar bidiyo, shugaban hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Lei Haichao, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da abokan huldarta na nahiyar Afirka, wajen bunkasa tsarin kiwon lafiyar al’umma, da fadada hadin gwiwa a fannonin da suka hada da na shawo kan cututtuka masu yaduwa, da kiwon lafiyar mata masu ciki da kananan yara.
A nasa tsokaci kuwa, ministan lafiyar kasar Tunisiya Mustapha Ferjani, cewa ya yi dandalin na da nufin gina wani salon kawance na bai daya tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya ce kasarsa ta shafe tsawon lokaci a matsayin gadar dake hade Sin da Afirka a fannin hadin gwiwar kiwon lafiya, inda tun a shekarar 1973, Sin ta fara tura tawagar jami’an lafiya na Sin domin gudanar da ayyuka a kasar. Mista Ferjani ya bayyana dandalin a matsayin wata dama mai inganci, ta hade kwararru na Tunisiya, da kwarewar Sin a fannin kimiyya, da burikan kasashen Afirka na bunkasa kiwon lafiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














