ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Bude Sabon Babi A Yankin Hong Kong

by CMG Hausa
4 years ago
Hong kong

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Sanin kowa ne cewa, kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya. Kuma tun bayan da yankin musamman na Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, bisa ka’ida ta 23 cikin babbar dokar yankin, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta dankawa yankin izinin kafa dokarsa ta fannin kiyaye tsaron kasa. 

Sai dai kafin kammala aikin kafa dokar, yankin ya fuskanci wasu ’yan hatsaniya, na rashin doka a bangaren tsaron kasa, wanda masana ke cewa, ba ya rasa nasaba da tsoma baki cikin harkokin yankin daga ketare.

  • Majalisar Gudanarwar Sin Ta Nada Sabbin Jami’an Gwamnatin HKSAR

Duk mai bibiyar al’amuran yau da kullum, ya ga yadda a ’yan shekarun baya-baya, wasu bata-gari suka yi yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari da tutar kasa, da zuga al’umma don su mamaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai harin kan mai uwa da wabi, da cin zarafin ‘yan sanda wadanda a kullum suke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaron al’umma, al’amuran da suka kasance ayyukan ta’addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa. Kuma duk wata kasa da ta san abin da take yi, ba za ta amince da irin wannan danyen aiki ba.
Kamar kowace kasa mai cikakken ’yanci, ita ma kasar Sin tana da ’yancin kafa dokokin da za su dace da yanayi da ma tsarin tafiyar da cikakkun yankunanta. Kuma tun lokacin da aka kafa, tare da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, wadda wata muhimmiyar dama ce ta yanke hukunci ga baragurbin dake neman ta da rikici a yankin, lamarin da ya tabbatar da ci gaba mai dorewa a yankin, da ma tafiyar da tsarin nan na kasa daya amma tsarin mulki iri biyu yadda ya kamata.
Jagororin yankin dai sun sha nanata cewa, masu bin doka suna maraba da dokar tsaron da aka kafa, matakin da ya kara janyo masu sha’awar zuba da neman halaliya tare da kara dawo da martabar yankin a idon duniya.
Yanzu dai yankin Hong Kong ya zabi shugabanni masu kishin kasa, wadanda za su fara aikin jan ragamar harkokin yankin daga ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara. Matakin da masu sharhi ke cewa, ya bude wani sabon babi a yankin, tun bayan da aka kafa sabbin dokokin tsaron kasa da na zabe masu alaka da yankin.
Burin kowace kasa mai ’yanci dake da kishin muhimman muradun al’ummomin ta, shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a maimakon zangar-zangar da za ta kai ga koma bayan kasa da al’ummarta a dukkan fannoni. Kuma kowa da irin kiwon da ya karbe shi.
Duk wata kasa mai cikakken ’yanci, wajibi ne tana da dokar tsaron kasarta. Kuma duk wanda ya karya doka, tilas ne doka za ta taka shi. Da ma “Icce aka ce, tun yana danye ake lankwasa shi”. (Ibrahim Yaya)

ADVERTISEMENT
Hong kong
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka’idojin Zaben 2023

INEC Ta Tabbatar Da Cafke Jami'inta Da Ke Karbar Na Goro Yana Wa Jama'a Rijistar Zabe A Ribas

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.