A yayin da ake daf da “ranar kare kwararowar hamada da fari ta duniya” karo na 29, wadda ta kan fado a ranar 17 ga watan Yunin kowace shekara, a hannu guda kuma an gudanar da taron dandalin hamadar Taklimakan a birnin Korla na jihar Xinjiang ta kasar Sin tun daga ranar 9 har zuwa 12 ga wata.
An gudanar da taron ne da nufin raba fasahohi masu inganci na kasar Sin ta fannin kare kwararowar hamada ga kasashen dake da bukata, don inganta hadin gwiwa da mu’amala a tsakanin kasar Sin da ma kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” wajen yaki da kwararowar hamada, tare da yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su mai da hankali a kan matsalar kwararowar hamada, musamman ma fito da shirye-shiryen da suka dace wajen daidaita matsalolin kwararowar hamada da ake fuskanta a sassan tsakiyar Asiya da yammacin Asiya da kuma Afirka.
Sashen nazarin yanayin halittu da bayanan kasa ta jihar Xinjiang karkashin cibiyar nazarin harkokin kimiyya ta kasar Sin da sakatariyar kungiyar shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall (PAGGW) da sauran wasu sassa ne suka hada gwiwa wajen gudanar da taron, kuma jami’an gwamnati da masana kusan 180 ne suka halarci taron, ciki har da baki sama da 40 da suka zo daga kasashen Asiya da kuma Afirka. (Lubabatu)