Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar rashin amincewar kasar Sin da adawarta, ta kuma gabatar da korafi ga tsagin Amurka, dangane da kudurin dokar tsaron kasar ta Amurka.
Guo ya yi tsokacin ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, inda ya shaidawa ‘yan jaridu cewa dokar tsaron kasar Amurka ta 2026, ta zuzuta batun kasancewar Sin barazana ga Amurka, ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kana ta illata ikon mulkin kai, da tsaro, da moriyar ci gaban kasar Sin.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta kauracewa sanya wasu sassa na muzgunawa kasar Sin cikin kudurin dokar, ta kuma kawar da duk wani matsin lamba da ka iya yin mummunan tasiri. (Saminu Alhassan)














