Al’ummar Unguwar Muchila da ke karamar Hukumar Mubi ta Arewa a Jihar Adamawa, sun roki ‘yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da su binciki harin da aka kai wa ayarin motocin matar Gwamnan Jihar, Hajiya Lami Fintiri a yankin.
Mista Sunday Mathew, mai magana da yawun al’ummar ne ya yi wannan kiran a ranar Talata a wani taron manema labarai a Yola.
- Gwajin Dawo Da Rukunonin Yawon Bude Ido Zuwa Kasashen Ketare Da Sin Ke Yi Zai Farfado Da Kasuwar Yawon Bude Ido Ta Duniya
- Kasar Sin Ta Kasance Mai Hangen Nesa Da Samarwa Kanta Mafita A Duk Lokacin Da Ake Mata Zagon Kasa
Ya ce ziyarar da uwargidan gwamnan ta kai a ranar 4 ga watan Fabrairu, ba ta siyasa ba ce, face gayyata da matan Katolika suka yi domin halartar taronsu.
A cewarsa, wasu bata gari ne suka kai hari kan ayarin motocin inda suka lalata motoci hudu ciki har da wata motar ‘yan jarida.
“Don haka ne muka taru domin yin kira ga kwamishinan ‘yansanda da daraktan tsaro na jihar da su gudanar da cikakken bincike.
“Kuma, don tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka aikata laifin da masu daukar nauyinsu a gaban kuliya,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga mutanen kirki a yankin da wadanda abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu su kasance masu bin doka da oda. Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa doka za ta yi maganin duk wanda ke da hannu a harin.