Kotun kolin ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga hana kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudi daga ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.
Jihohin Arewa uku – Kaduna, Kogi da Zamfara ne – suka shigar da karar a ranar 3 ga watan Fabrairu, inda suka bukaci kotun koli da ta dakatar da manufofin sauya fasalin Babban Bankin Nijeriya (CBN, ) ya yi wa Naira.
- An Bukaci DSS Ta Yi Bincike Kan Kai Wa Ayarin Motocin Matar Gwamnan Adamawa Hari
- Jami’in DSS Na Bogi Da Wasu Sun Shiga Hannu A Osun
Kwamitin mutum bakwai na kotun koli karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro, a cikin hukuncin da aka yanke, ya ba da umarnin wucin gadi na hana Gwamnatin Tarayya da CBN da kuma Bankunan kasuwanci daina karbar tsohon kudin dava ranar 10 ga Fabrairu, wa’adin tsohon kudin Naira 200, 500 da 1000.
Kotun ta kara da cewa, CBN, bankunan kasuwanci ba za su daina karbar kudin ba har sai an yanke sanarwar kan hukuncin da za ta zartat a ranar 15 ga Fabrairu.
Wannan dai na zuwa ne bayan canjin kudi da CBN ya yi wanda ya haifar da yamutsi a tsakanin mutane.