Farfesa a bangaren kimiyyar aikin noma a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Ibrahim Haruna, ya bukaci manoma su rungumi tsarin noma na kimiyyar zamani da ke jure wa sauyin yanayi.
Ya bayar da wannan shawarar ce a taron gabatar da kasida na jami’ar karo na 33 da aka gudanar a Karamar Hukumar Keffi da ke Jihar Nasarawa.
- Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji
- Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
An gudanar da taron ne, kan batun sauyin yanayi, musamman kan yadda amfanin gonar da aka shuka, zai kasance yana jurewa kowane irin sauyin yanayi na noma.
A cewar Haruna, afkuwar sauyin yanayi, babbar barazana ce ga amfanin gonar da aka shuka, inda ya sanar da cewa; saboda haka, akwai bukatar manoma su rungumi tsarin noma na kimiyyar zamani da ke jure wa sauyin yanayi, domin kare amfanin gonar da suka shuka daga lalacewa, domin cimma burin da ake da shi na samar da wadataccen abinci a kasar.
Ya kara da cewa, afkuwar sauyin yanayi, na jawo lalacewar amfanin gonar da aka shuka, musamman duba da yadda kalubalen ke afkuwa a fadin duniya.
Ya ci gaba da cewa, rungumar wannan tsari; zai kuma taimaka wajen yakar yunwa a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa; ana aiwatar da wannan dabarar yakar sauyin yanayi ne ta hanyar yin amfani da dabarun noman gargajiya, wato yin amfani da takin gargajiya da sauyawa daga gonar da aka yi noma zuwa wata gonar daban.
Sauran dabarun ya bayyana cewa, sun hada da yin shuka da ingantaccen Irin noma da kuma yin noman rani.
Kazalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya wannan tsari ya zama na kasa baki-daya da za a rika yin amfani da shi.
Shi ma a nasa jawabin a wajen taron, Shugaban Jami’ar Farfesa Suleiman Bala-Mohammed ya ce; kasidar da aka gabatar a wajen taron ta zo a kan gaba, musamman duba da cewa; ana magana ne a kan yadda za a samar da wadataccen abinci a kasar da kuma wanda za a fitar zuwa ketare.














