Rundunar Ƴansandan Metropolitan ta Birtaniya ta bayyana cewa ta kama kuma ta gurfanar da babban wanda ake zargi, Andre Wright-Walters, bisa zargin kisan wani ɗan Nijeriya mai shekara 67, James Gbadamosi.
Jaridar PUNCH Metro ta rawaito daga wata sanarwa da ƴan sandan Metropolitan suka fitar a ranar Litinin cewa an kai wa Gbadamosi hari tare da dukan sa a ranar 24 ga watan Agusta a Ballam High Road da misalin ƙarfe 4 na yamma, lamarin da ya jawo masa munanan raunuka masu barazana ga rayuwa.
- An Sake Daure Dan Nijeriya Shekara Biyar A Birtaniya Kan Laifin Fyade
- Iran Ta Zargi Birtaniya, Faransa, Da Jamus Da Gazawa Kan Yarjejeniyar Nukiliyar 2015
Bayan samun wannan bayani, jami’an ƴan sanda suka dira wurin da aka kai harin a Balham High Road, suka garzaya da Gbadamosi zuwa asibiti.
Sanarwar ta nuna cewa, duk da haka, Gbadamosi ya kasa jure raunukan da ya samu inda ya rasu a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce, “An kira ƴan sanda bayan rahoton cewa an kai wa wani mutum hari a Balham High Road da misalin ƙarfe 3:40 na rana a ranar Lahadi, 24 ga Agusta.
Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.”
Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari a watan Agusta, amma aka ba da belinsa.
Sai dai an sake kama shi a ranar Asabar bayan rasuwar Gbadamosi, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare a ranar Litinin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Andre Wright-Walters, mai shekaru 37 (05.02.1988) na Aɓery Hill, Greenwich, an gurfanar da shi a ranar Lahadi, 7 ga Satumba. Ya bayyana a gaban kotun majistare ta Wimbledon a ranar Litinin, 8 ga Satumba. An kama Wright-Walters bisa zargin kisa a ranar Asabar, 6 ga Satumba.”
“A baya an riga an gurfanar da shi a ranar Laraba, 27 ga Agusta, bisa zargin yin mummunan lahani da gangan da kuma mallakar miyagun ƙwayoyi rukuni na A, bayan an kama shi a ranar da abin ya faru.
Ya bayyana a gaban kotun majistare ta Wimbledon a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, sannan aka sake shi a kan beli don sake bayyana a gaban kotun ƙoli ta Kingston-upon-Thames a ranar Laraba, 24 ga Satumba.”
Ƴansanda sun ƙara da cewa an kuma kama wani wanda ake zargin abokin haɗin gwiwa (ba a bayyana sunansa ba) bisa zargin da ya shafi kisan, amma aka ba shi beli yayin da ake ci gaba da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp